28 Nuwamba 2026 - 19:15
Source: ABNA24
Rahoton Hukumar Yaɗa Labarai Ta Waje Ta Yemen Kan Ta’addancin Saudiyya A Bani Hushaysh + Sunayen Shahidai Da Hotuna Masu Ratsa Zuciya

Hukumar kula da yaɗa labarai ta waje ta Yemen, ta wallafa wani rahoto na ɗan adam da na sharia game da laifin da Saudiyya ta aka aikata a ƙauyen "Al-Shariyah" da ke yankin Bani Hushaysh, a gabashin San'a.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Ranar 7 ga Nuwamba ta kasance wani sabuwar shafi ne da ya ƙaru a bakaken shafukan littafin laifuffukan ta’addancin gwamnatin Al Saud kan al'ummar Yemen da ta ke zalunta. Hukumar yaɗa labarai ta waje ta Yemen ta shirya rahoton wannan laifin da "jami'an Khadim al-Haramain!" suka aikata, tare da hotuna masu ratsa zuciya domin ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da al'ummar duniya su karya tare da dakatar da yin shirunsu a gaban wannan cikakken laifin yaƙi:

Da safiyar Asabar, 7 ga Nuwamba 2026 miladiyya a ƙauyen "Al-Shariyah" da ke yankin Bani Hushaysh (gabashin babban birnin, San'a), ta zamo safiya da ba a saba da ita ba. Yara suna wasa a farfajiyar gidajensu na laka da sauƙakka, mata suna shirya burodin tandanu don abincin rana kuma maza suna shirye-shiryen zuwa gonaki. Amma cikin wani ɗan lokaci, wannan kwanciyar hankali ta juya zuwa kururuwa da barna; jiragen maƙiyiya (Saudi Arabiya) sun kai hare-haren sama a jere waɗanda ba su bar ko dutse a kan dutse ba kuma cikin 'yan daƙiƙa kaɗan, sun mayar da gidajen zama shida masu aminci zuwa makabartun jama'a.

Rahoton Hukumar Yaɗa Labarai Ta Waje Ta Yemen Kan Ta’addancin Saudiyya A Bani Hushaysh + Sunayen Shahidai Da Hotuna Masu Ratsa Zuciya

Wannan ba yaƙi ne tsakanin sojoji biyu ba; a'a, mamayewa ce bayyananniya ga rayuwa da aminci; mamayewa ga dariyar yaro da bai cika shekarunsa ba, da rufin da aikinsa kawai shine kare iyali da ke ƙoƙarin rayuwa cikin mutunci a tsakiyar kawanya mai ci gaba.

Na Farko: Yayinda Ake Kashe Rayuwa Kuma Ake Bin Diddigin Da Tsorar Da Hannayen Masu Kawo Dauki

Laifin bai tsaya kan jefa bama-bamai kan gidaje a kan mazaunansu da tsakar rana ba, a'a ya kai ga har zuwa hana "damar ceto" garesu; domin jiragen yaƙi na maƙiyiya (Saudi Arabiya), a lokacin da mutane, ƙungiyoyin kawo dauki da ma'aikatan jinya da 'yan jarida ke gudu domin zuwa fitar da waɗanda abin ya shafa daga ƙarƙashin tarkace, sun sake jefa bama-bamai a wurin da suka kai hari na farko ya faru sau uku zuwa huɗu a jere. Haka kuma, sun kai hari kan hanyoyin da ke kaiwa ƙauyen don hana motocin agaji isowa. Maimaita jefa bama-bamai a kan tarkace da masu kawo dauki, yana nuni da rashin kulawa bayyananniya ga dukkan dabi'un ɗan adam da ƙoƙarin ƙara adadin waɗanda abin ya shafa da haifar da tsoro da firgici a cikin al'umma da suka yunkoro don taimaka wa juna.

A cikin waɗannan mintuna masu nauyi, wani iyali daga gidan "Al Al-Aghrabi," sun rasa mutane tara daga cikin membobinsu a lokaci ɗaya. Yaron da ya tsira, "Yusuf Salim," a lokacin da yake cike da raunuka da jin zafi, ya fito daga ƙarƙashin tarkace; ya kasance ƙaramin shaida ga babban bala'i da ya faru. Kwanaki da yawa bayan haka, a makabartar Bani Hushaysh, iyaye maza da mata sun tsaya kan kaburburan ƙananan 'ya'yansu; uba da ke bankwana da matarsa da 'ya'yansa uku da uwa da ke binne 'yarta mai shekaru huɗu; yanayin da ya girgiza zukata a babban taron jana'izar da ya fara daga Masallacin "Al-Sha'b" a San'a.

Rahoton Hukumar Yaɗa Labarai Ta Waje Ta Yemen Kan Ta’addancin Saudiyya A Bani Hushaysh + Sunayen Shahidai Da Hotuna Masu Ratsa Zuciya

Raunata membobin ƙungiyoyin agaji da na likita a lokacin fitar da waɗanda abin ya shafa daga ƙarƙashin tarkace.

Na Biyu: Adadin Lambobin Da Ke Nuni Da Bayar Da Labarin Irin Bala'in Yara Da Mata Suka Shiga

Ƙididdigar ƙarshe ta wannan kisan kiyashin da ma'aikatar lafiya da muhalli ta San'a da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam suka bayyana, tana fallasa wani zurfin rauni na ɗan adam; jimillar waɗanda abin ya shafa fararen hula 84 (shahidai 44 da raunuka 40) inda yara da mata ke tsakiyar hari:

- Shahidai yara 21: (tare da gwaomman yara da suka ji rauni); waɗanda ya kasance kusan rabin shahidan da aka kashe a cikin gidaje ko farfajiyar gidajensu; waɗanda suka yi shahada kafin su cika yarinta.

- Shahidai mata 10: (tare da gwomman mata da suka ji rauni); da yawa daga cikinsu sun shahada ne a lokacin da a cewar shaidun wadanda suke a wurin, suke ƙoƙarin kare 'ya'yansu da jikinsu a ƙarƙashin rufin gidajen da suka faɗi.

- Raunata ma'aikatan jin kai da yaɗa labarai: ciki har da masu ɗaukar hoto na tashar "Al-Masirah" (Ahmad da Abbas Jahhaf) waɗanda suka samu rauni a lokacin da suke gudanar da aikinsu wajen rubuta wannan kisan kiyashi da bayar da agaji ga waɗanda suka ji rauni.

- Rashin matsuguni da gudun hijira da lalacewar iyalai 52: a ƙauyen, sakamakon cikakken lalacewar gidajensu wanda ya kai ga hana su mafaka da muhimman buƙatun rayuwa a cikin mawuyacin yanayi na kawanya.

Rahoton Hukumar Yaɗa Labarai Ta Waje Ta Yemen Kan Ta’addancin Saudiyya A Bani Hushaysh + Sunayen Shahidai Da Hotuna Masu Ratsa Zuciya

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha